Saturday, January 2, 2021

Wata Amarya ta rasu awanni 3 kafin daura aurenta a Katsina

 



Innalillahi wa’inna ilaihir-raji’un
Labari ya karade shafukan sada zumunta cewa Allah ya yiwa Fatima Hassan Fari rasuwa wata amarya wacce ake shirin daura mata aure a safiyar yau Asabar.

Manuniya ta ruwaito za’ayi jana’izar margayiyar karfe 2:00 na ranar yau.

Fatima ta rasu awanni uku gabanin auren ta a karamar hukumar Funtua jihar Katsina






No comments:

Post a Comment

Pages