Thursday, October 5, 2017

Makarfi yayi magana a kan takarar shugabancin kasar Fayose


Makarfi ya bayyana cewar neman takarar shugabancin kasar Fayose ya sabawa shawarar jam'iyyar PDP - Makarfi yayi watsi da jita-jitar cewar wai PDP zata bawa Atiku takara matukar ya amince ya dawo jam'iyyar - Jam'iyyar ta bayyana cewar dan takarar ta daga arewa zai fito Shugaban rikon kwarya na jam'iyyar PDP, Sanata Ahmad Makarfi, ya bayyana cewar neman takarar shugabancin kasar gwamnanan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya sabawa shawarar jam'iyyar PDP. Makarfi ya bayyana haka ne jiya a Kaduna yayin wata ganawa da manema labarai.

Makarfi ya ce "Shi, Fayose, yayi gaban kansa ne kawai, amma bada sahalewar jam'iyya ya kaddamar da takarar sa ba. Matsayin jam'iyyar PDP na fitar da dan takarar shugabancin kasa daga arewa bai canja ba". Hakazalika Makarfi yayi watsi da jita-jitar cewar wai PDP zata bawa Atiku takara matukar ya amince ya dawo jam'iyyar.
Ayodele Fayose dai ya kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a karkashin jam'iyyarsa ta PDP a zaben shekarar 2019 duk da cewar jam'iyyar ta bayyana cewar dan takarar ta daga arewa zai fito.

No comments:

Post a Comment

Pages