Tuesday, August 29, 2017

Jerin dukiyoyin da tsohuwar ministan mai, Diezani Alison-Madueke, ta handama


Jerin dukiyoyin da tsohuwar ministan mai, Diezani Alison-Madueke, ta handama Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta hanyar hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta zage dantse wajen yakan wadanda suka jiwa tattalin arzikin Najeriya rauni Bayan garkame tsohon NSA, Sambo Dasuki, wanda ya handami kudin makamai $2bn, tsohuwar ministan man fetur, Diezani Alison Madueke, tayi mumunar raunata tattalin arzikin Najeriya. Amma tun kafin shugaba Buhari ya hau mulki ta arce kasar Landan. Ga jerin kudaden da aka gano zuwa yanzu: 

1) Wadanda aka kwace din-din-din $153Million (kudi a hannu) Gida kimanin kudi $37.5 $2.7 Million (kudi a hannu) N84.5 Million (kudi a hannu) N7.6 Billion (kudi a hannu). 

2) Kwacewan wucin gadi Dukiyan $22 Million (Gidaje 56)

 3) Wadanda gwamnatin Birtaniya ta kwace: £9.8Million

 4) Wanda EFCC ke shirin daskararwa: $20.15M Dukiya a Dubai. Jimilla: $155.7Million (kudi a hannu) $79.65 Million (dukiyoyi) £9.8 Million (dukiyoyi) N7.684.5Billion (kudi a hannu) Jimilla a kudin Najeriya - N94.8Billion ** Farashin canjin da akayi amfani da shi $ - N350 £ - N460

No comments:

Post a Comment

Pages