Abin da ya sa na dawo tare da album biyu ~ Nura M Inuwa
NURA M. Inuwa shahararren mawaƙi ne na wannan zamanin. Ya shahara a fagen rubutawa da rera waƙar soyayya da ta biki da ta siyasa. A fagen waƙar soyayya, kafin ka samu wanda ya kai shi iya shirya zance mai sarƙaƙiya tare da jan hankali da jefa mai saurare cikin kogin tunani, sai ka tona sosai.
Wani abu game da Nura shi ne a duk shekara ya kan fitar da faifan waƙoƙin sa aƙalla guda biyu. To, sai kuma aka samu akasi, wannan sha’iri ya shafe shekara biyu ba a ga wani sabon album daga gare shi ba, abin kamar an yi ruwa an ɗauke.
Hakan ya janyo maganganu iri-iri daga wajen jama’a, tare da damuwa da ƙorafi daga masoyan sa.Sai da ta kai wasu masoyan sa su ka yi zanga-zangar lumana zuwa ofis ɗin sa a Kano domin isar da kukan su a gare shi. A ganin su, ya za a ce hamshaƙin mawaƙi kamar Nura ya daɗe bai share musu hawaye ba? Wannan zanga-zanga ita ce irin ta ta farko da aka gudanar ga wani mawaƙi a masana’antar Kannywood.
To, Nura M. Inuwa dai ya amsa kiran su, domin kuwa a cikin wannan makon ya bada sanarwar cewa zai fitar da sababbin kundayen waƙoƙin sa guda biyu. Har ya nuna fostar waɗannan album ɗin a Instagram.
Mujallar Fim ta ziyarci fasihin a ofis ɗin sa jiya Talata, 16 ga Fabrairu, 2021 inda ta tattauna da shi kan wannan yunƙuri nasa na share wa masoyan sa hawaye da abubuwan da su ka wakana kafin lokacin, da kuma abin da ya ƙudurta nan gaba. Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance:
FIM: Malam Nura, an ɗauki tsawon lokaci ba tare da an ga ka saki sabon kundin waƙoƙin ka ba. Me ya sa?
NURA M. INUWA: Abin da ya sa ba a ganin sabbin waƙoƙi na ko album ɗi na shi ne wannan na daga cikin tsarin tafiya ta a cikin sabgar waƙa. Kuma tun kafin a kawo yanzu na riga da na tsara haka da za a zo wani lokaci wanda zan ɗan tsaya in ɗan huta domin na san cewa waƙa ba wai abinci ba ce da za a ci yau a ci gobe. To ka ga ya kamata in an ɗan tafi an huta kamar yadda na yi yanzu, to in ɗan bada hutu na ɗan wani lokaci domin masu sauraro su sarara ni ma kuma in samu in sarara sannan kuma in dawo in ɗora daga inda na tsaya idan Ubangiji ya nufa.
FIM: A baya an riƙa raɗe-raɗin wai asiri aka yi maka, wai dalilin da ya sa ka kasa waƙa kenan. Me za ka ce kan haka?
NURA M. INUWA (dariya): Ni a cikin tsarin rayuwa ta kuma daga cikin abubuwan da ban fiya ɗauka ba duk da an ce gaskiya ne ni ban yarda a ce an yi mani asiri kuma in ɗauka. Daga cikin abin da na ke damuwa da shi shi ne abubuwan da na sa a gaba ko na tsara zan yi shi ne abin da na fi maida hankali a kai kuma shi na ke yi.
FIM: Duk da cewa a wannan shekarar za ka fitar da kundayen waƙoƙin ka har kala biyu, shin ko waɗannan album ɗin naka waƙoƙi nawa-nawa su ka ƙunsa?.
NURA M. INUWA: To kundin waƙoƙin da zan fitar guda biyu sun haɗa da ‘Ni Da Ke (Me and You)’ da kuma ‘Lokaci’.
Shi dai album ɗin ‘Ni Da Ke (Me and You)’ ya ƙunshi waƙoƙi 17, shi ma album ɗin ‘Lokaci’ zai ɗauki kimanin waƙoƙi 14 saboda waƙoƙin sun fi nauyi da kuma tsawo.
FIM: Yaushe waɗannan album ɗin za su fito?
NURA M. INUWA: Har zuwa yanzu ba mu sa rana ba, amma dai mun ce ƙarshen watan nan in Allah ya kai mu. Kawai masoyan mu su jira zuwa ƙarshen watan nan.
FIM: Harkar album babu riba saboda rashin kasuwar sidi da kuma satar basira. Ya za ka yi wajen cinikin sa har ma ka ci riba?
NURA M. INUWA: Zan ci riba ne bisa yadda al’amura su ka canza. Zan yi amfani da duk hanyoyin da ake bi a ɗora a yanar gizo, za mu yi mu ma. Sannan za mu dawo hanyar da ake cewa kamar an bar ta; kuma ba barinta aka yi ba, wani lokacin tsallen da mu ke saurin yi ne ya ke sa mu ga kamar an bar wani abin. To za mu gwada ita kan ta wannan hanyar. Misali da yanzu mu na ɗaukar masoya na sun isa su riƙe ni shi kenan za ka ga cewa wannan ga inda ya zaɓa ya yi cinikin sa na hajar sa, ni ma kuma ga inda na zaɓa. To in dai masoyan sa za su yi sadaukarwar nan ta cewa mu ga namu inda ya bi kuma mu na yi ne don shi kuma ya ƙaru, to ka ga idan ma ban ɗora a yanar gizo ba in ce ni iya sidi na ke so, ka ga kenan masoya na ta nan za su saya, kuma ta nan za su sa na ƙaru. Kai ko mutum saya ya yi, in ya ɗauki abin da zai ɗauka zai iya ɗauka in na yarda sidin zai yi an dai ƙaru. Hakan kuma da na yi ni na zaɓa da kuma mutane sun san da haka da ba su damu kan su wajen furta cewa an bar hanya ko makamancin haka.
FIM: Shin ko za ka yi bidiyon waƙoƙin ne ka ɗora su a YouTube kamar yadda wasu mawaƙan ke yi?
NURA M. INUWA: Za mu duba daga baya mu ga dacewar waɗanda ya kamata mu ɗan taɓa kasancewar akwai buƙatar hakan daga masoya. Saboda na daɗe ban yi wani abin da ya shafi bidiyo ba da za su gani.
FIM: Me za ka ce wa masoyan ka da su ka daɗe su na jiran wannan tagwayen album ɗin, har ma da waɗanda su ka yi zanga-zanga?
NURA M. INUWA: Ina mai daɗa ba su haƙuri da su kwantar da hankalin su, wannan hutu da na yi yanzu na dawo aiki bakin rai bakin fama. Zan ci gaba da nishaɗantar da su cikin yaddar Ubangiji, kamar yadda ba su gaza wajen bibiya ta da kuma damuwa a kan abin ba, in-sha Allahu yanzu ni ma ba zan yi ƙasa a gwiwa wajen faranta musu ba, in-sha Allah.
FIM: Shin sakamakon zanga-zangar ne ya sa za ka saki waɗannan album ɗin?
NURA M. INUWA (dariya): A’a, abin dai da man shiri ne kamar yadda na faɗa, na tsara haka. Sai dai kuma su mutane da ba su sani ba ban musu bayani ba na ga abin da da ya ke akwai ba, shi ya sa ya zama sun kasa haƙuri. Gani su ke kamar na ma bari gaba ɗaya, ba zan ci gaba ba, shi ya sa kuma su ka yi zanga-zanga. Amma da su ka ji batun cewa da man dai akwai shirin da na ke yi, na san sun samu gamsuwa da nutsuwa sannan hakan ni ma ya saka min wani ƙwarin gwiwa wajen yin ƙoƙarin in yi in yi in kawo wannan abin, saɓanin yadda na dawo ina ɗan tafiya a hankali, to yanzu na ƙara azama dalilin wannan zanga-zanga.
FIM: Yanzu kuma sai zuwa yaushe za ka sake yin wani album ɗin? Ko sai bayan shekara biyu kuma?
NURA M. INUWA: A’a, ba haka ba ne. Za mu gani in dai mu ka saki waɗannan album ɗin, hankalin masoya na ya kwanta, zan kuma yin tunani in ga me kuma zan tunkara a gaba ɗin. Amma dai wannan ina kan ra’ayi na na in ga na kwantar musu da hankali da waɗannan waƙoƙin da za su fito, in sun fito kuma an samu wannan nutsuwar da gamsuwar, ni kuma zan yi tunanin me ya kamata na yi a gaba. Zan iya tafiya sai wani lokacin ɗin ko kuma bai kamata in tafi ba, duk dai zan ga me ya kamata in-sha Allahu.
FIM: Da me za ka ƙarƙare a ƙarshe?
NURA M. INUWA: Da fari ina godiya da wannan mujallar da ta ba ni dama na isar da saƙo na ga masoya na na abubuwan da ba su sani ba game da ni; ina godiya sosai. Allah ya ƙara ɗaukaka.
Sannan ina godiya ga masoya na bisa ƙwarin gwiwar da su ke ba ni, ita ta ɗauko ni ta kuma kawo ni wannan matsayi da na ke kai a yanzu. Ina godiya, Allah ya saka da alkairi, ya bar zumunci da soyayya da kuma ƙaunar da ke tsakanin mu.
![Nura M. Inuwa Nura M. Inuwa](https://i1.wp.com/fimmagazine.com/wp-content/uploads/2021/02/tmp-cam-1507208165.jpg?resize=640%2C326&ssl=1)
No comments:
Post a Comment