Thursday, February 11, 2021

'Yan fashi sun kashe wani ango wata daya bayan aurensa

 




Wata matar da aka kashe mijinta ta bayyana yadda 'yan fashi suka mayar da ita bazawara

 - Tace, 'yan fashin sun afkawa gidansu cikin dare daga bisani suka harbe mijinta

 - Ta kuma bayyana yadda aka cafke wadanda suka aikata mummunan aikin kashe mijin nata Wata matar mai suna Ramatu Idris da ke Unguwar Malam Lamu, Tankarau, Unguwar Dutsen Abba da ke karamar Hukumar Zariya, ta bayyana yadda ’yan fashi suka sanya ta zama bazawara bayan wata daya da aurenta da marigayi Yusuf Suleiman.


 Idris ya fadawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Alhamis cewa lamarin ya faru ne a ranar 4 ga Fabrairu, da misalin karfe 12:45 na rana, kwanaki 28 bayan aurenta da Suleiman, The Nation ta ruwaito. “Sun kasance kusan su bakwai ('yan fashin). 

Sun afka cikin gidanmu da karfi rike da bindigogi da sanda. 


 “Ni da mijina mun je ganin abin da ke faruwa a kan jin hayaniya da ihun neman taimako, sai kawai aka harbe shi a wuya a gabana kuma ya mutu nan take. 

Ramatu, wanda lamarin ya rutsa da ita, ta yi ikirarin wadanda suka kashe mijinta masu aikata laifuka ne da suka kai samame gidan Alhaji Abdulaziz Sani, Kansilan da ke wakiltar Unguwar Dutsen Abba, suka yi awon gaba da ’yan uwansa shida. 

Ta ce daga baya ne jami'an hukumar kula da sintiri na jihar Kaduna (KADVS) suka samu nasarar cafke 'yan fashin a kauyen Unguwan Mai Turmi, da ke karamar hukumar Igabi.

 A halin da ake ciki bayan harin da aka kaiwa gidan Sani da kisan Suleiman, mazauna Kampani da Saye a Unguwar Dutsen Abba, sun roki Gwamnatin Jihar Kaduna da ta tura karin jami’an tsaro a kan hanyoyi a yankin don magance satar shanu, satar mutane da sauran laifuka. 



No comments:

Post a Comment

Pages