- Majalisar dattawa ta gayyaci masu ruwa da tsaki kan harkar kudade a Najeriya kan kudin intanet
- Majalisar, ta gayyaci har da gwamnan Babban Bankin Najeriya don bada bayanin kan haramta kudin
- Majalisar ta bayyana cewa ya kamata a zauna a fayyace menene usulubin haramta kudaden intanet din Majalisar dattijai, a ranar Alhamis, ta umarci kwamitinta na Banki, Inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi, da su gayyaci Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele da Darakta-Janar na Hukumar Tsaro da Musayar Lamido Yuguda, don tattaunawa kan kudin intanet.
Don tattauanawa da Kwamitin Banki da Kudin da Sanata Uba Sani ke jagoranta ana gayyatar Kwamitocin Fasahar Sadarwa da Sadarwa da Cin Hanci da Rashawa da Kasuwar Hannun Jari, tare da Sanata Yakubu Oseni da Ibikunle Amosun a matsayin shugabanni.
Kudurin ya biyo bayan umarnin CBN na dakatar da cibiyoyin kuɗi daga yin ma'amala da kudaden intanet, Nigerian Tribune ta ruwaito.

No comments:
Post a Comment