Alhaji Lateef Jakande ya yi rayuwa dan jin dadin jama'a ba kansa ba, Buhari yayi alhinin mutuwarsa
Shugaba Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan tsohon gwamnan jihar
- Alhaji Jakande ya mulki Legas kafin Buhari ya cire shi bayan juyin mulkin 1979
- Jam'iyyar PDD da Atiku sun yabawa marigayin bisa ayyukan da yayi Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar gwamnan farko na farin hula na jihar Legas, Alhaji Lateef Jakande, ya siffantashi matsayin wanda yayi rayuwa don jin dadin wasu ba kansa ba. Mai magana da yawun Buhari Femi Adesina, ya bayyana cewa Buhari ya yi rayuwa mai albarka mai cike da darruus
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da hakan a shafinsa na Tuwita ranar Alhamis.
Ina mai sanar da mutuwar mutumin kirki, babban dan siyasa, kuma gwamnan jihar Legas na farko, Alhaji Lateef Kayode Jakande," Sanwo Olu yace.

No comments:
Post a Comment