Shugaban yan bindiga a Zamfara, Auwalu Daudawa ya bayyana dalilin da yasa ya mika wuya ga gwamnati
- Daudawa ya ce ya gano cewa hare-haren bata da amfani kuma babu riba a cikin harkar
- Daudawa ya kuma ce wasu sauran yan bindigan za su bi sahunsa su mika wuya ga hukumomin tsaro Babban kwamandan yan bindiga a Zamfara mai suna Auwalu Daudawa ya ce ya amince ya mika bindigunsa ne bayan ya gano kai hare-hare babu riba kuma bata da amfani, Daily trust ta ruwaito. Daudawa na daya daga cikin wadanda ke jagorantar yan bindiga da ke dajin Dumburum a karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
Daudadawa ya sanar da hakan ne a ranar Talata a hedkwatar yan sanda da ke jihar Zamfara a Gusau, babban birnin jihar.
Ya ce ya yi imanin cewa wasu yan bindigan a dazukan Zamfara suma za su bi sahunsa su mika wuya domin dama suna neman irin wannan damar. "Yan banga da ake fi sani da 'yan sakai suna matsa mana.
"Hakan ne yasa muka dauki makamai amma duk da hakan ba su dena matsa mana ba.
Idan yan sakai (yan banga) suka cigaba da kashe fulani a kasuwanni da wasu wurare ba tare da shari'a ba ina baka tabbacin ba za a taba samun zaman lafiya ba. "Amma mun goda wa Allah saboda shiryar da mu kan hanya madaidaiciya," in ji shi.
Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba. Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

No comments:
Post a Comment