Tsoro da Rashin Gaskiya Ne Yasa Malaman Izala sunka Fara Janyewa Daya Dayan Daya Muqabala Da Abduljabar ~ Yaran Abduljabar
Wannan wani rubutu ce da yana Abduljabar sunka fara jindadi akan jin malam izala su biyu sheikh Aminu Ibrahim daurawa da Sheikhh Dr Ahmad Gummi.
Shiyasa sunka fara jindadi akan cewa sune bisa Gaskia wanda sunyi rubutu a shafinsu kamar haka.
“MAQARYATA NE, MAHA’INTA NE KUMA MAYAIDARANE, SUN NEMAN GUDUWA NE DAGA MUQABALA SHIYASA SUKE AIKO MAQARYATA GIDAJEN REDIYO DOMIN SU KADAR DA TUNANIN KU.
Dayawun duk dan Makarantar Mujamma’u Ashabil Kahfi Warraqeem Nigeria muna shelantawa Duniya Zaman Muqabala tsakanin Maulana Sheikh Dr Abduljabbar Kabara (H) da Majlisar Malaman Kano yana nan daram ba fashi, don haka kuyi watsi da duk wata propaganda da ake yadawa Akan wai Sheikh Dr Abduljabbar Kabara (H) yana neman salihu akan kar ayi zaman Muqabala da shi, qarya suke yi saboda basu da gaskiya ko ta redin farce, shi dama maqaryaci baya jin kunyar yayi qarya sabda baya tsoron gamuwarsa da Allah a ranar gobe.
Wadannan mutane da ake cewa Majlisar Malaman Kano, sune suke neman guduwa shi yasa suke rainawa mabiyan su hankali, kar su gane gazawar su a hujjatayya ta ilimi, su da kan su sun sani gaba dayan su maqaryata ne tun a Duniya kafin aje Lahira, shine suka za6i suji kunya Lahira akan ta Duniya, cikin ikon Allah sai gashi tun Aduniya Allah yana kunyata su, kowa yana gani.
JAN HANKAI:-
Bazai yiyu ba ace wadannan mutane da ake cewa Malamai suje wajen Gwamnati Kano suna yin sharri da qage da 6ata sunan Malam Abduljabbar (H), da sunan yana zagin Sahabbai ba tare da Hujja ba, kuma Gwamnatin tace su fito su zauna Muqabala da shehin Malamin (H) sanan su koma suna qarairayin don su sami damar guduwa, tabbas ya zama wajibi lallai ku mabiyan su ku tilasta musu akan su fito ayi wannan zaman (Muqabala) kamar yadda Gwamnatin kano ta shelantawa da Duniya, kuma kowa yaji da kunnen sa.
A qarshe muna cewa tsakanin mu da su wanda yake tsoron zama da zillewa a kan kar a zauna muqaba Allah ya tsine masa Albarka Duniya da Lahira, mu munce Ameen, suma wadannan malaman ko mabiyansu idan sun isa suma suce Ameen.
AKNM.
13/2/2021.”

No comments:
Post a Comment