NAIJ.com ta samu kuma haka zalika cewa jumillar tsayin hanyoyin idan aka kammala su zai kama kimanin ma'aunin tsawo na kilomita 3,421. Haka ma dai kamar dai yadda daftarin ya kunsa, hanyoyin jiragen kasar za su bi ne ta jihohin Lagos, Oyo, Osun, Ogun, Benin, Abuja, Kogi, Onitsha da Sokoto.
Kamar kuma yadda muka samu shine cewa hanyoyin da za'a fara shinfidawar sune na Lagos-Sagamu-Ijebu Ode-Ore-Benin City; sai Lagos-Ibadan-Osogbo-Baro-Abuja; sai kuma Ajaokuta (Eganyin)-Obajana-Jakura-Baro-Siraj-Abuja da kuma Ajaokuta zuwa Otukpo. Haka ma dai akwai Zaria-Kaura Namoda-Sokoto-Ileila-Birnin Koni a Niger Republic da dai sauran su.
No comments:
Post a Comment