- Abdulrasheed Bawa zai fuskanci shari'a dangane da nadin sa a matsayin shugaban EFCC
- Wani masanin shari'a, Osuagwu Ugochukwu, ya yi jayayya cewa akwai takaddama game da nadin Bawa
- Har yanzu Shugaban EFCC din bai yi martani ga matakin da kotu ta dauka ba Yanzu haka ana shari’a a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan batun zabar Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) Jaridar Guardian ta ruwaito cewa wani lauya, Osuagwu Ugochukwu, ya gabatar da karar da ke kalubalantar nadin Bawa don ya shugabanci hukumar.
Lauyan ya nemi kotun da ta yanke hukunci kan ko Bawa ya cancanci a nada shi shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa. Ya kuma bukaci kotu da ta yanke hukunci kan ko majalisar dattawa tana da hurumi a cikin doka don tabbatar da nadin Bawa, wanda ya yi ikirarin cewa ana ganin ya gaza da abin da ake bukata na sassan dokar da ta kafa EFCC.
Kotu ta ba majalisar dattawa da Bawa kwanaki 30 su tabbatar da dalilin da zai sa nadin ya dore.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa an bawa majalisar dattawan Najeriya takardar kotu game da karar.
A gefe guda, lauya mai kare tsohon mukaddashin shugaban EFCC, Tosin Ojaomo, ya ce ba ayi adalci a game da lamarin Ibrahim Magu da wasu abokan aikinsa ba.
Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa, Tosin Ojaomo, ya yi wannan magana ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin a ranar Larabar nan. Lauyan ya na magana ne a kan kwamitin binciken da shugaban kasa ya nada karkashin Ayo Salami domin a gano gaskiyar zargin da ke kan wuyan Magu.

No comments:
Post a Comment