Saturday, February 20, 2021

Yanzu Yanzu: FG ba za ta biya kudin fansa don sakin daliban Kagara ba - Lai Mohammed

 




- Kada wadanda suka yi garkuwa da yaran makarantar Kagara su yi tsammanin samun kudin fansa a cewar Lai Mohammed 

- A cewarsa, masu aikata laifin suna aiki ne a kan tunanin mutane ta hanyar sace mata da kananan yara 

- Ya kara da cewa gwamnati ba za ta bayyana dabarun ta na dawo da yaran ba Gwamnatin tarayya ba za ta biya kudin fansa ba wajen neman sakin dalibai da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, Kagara da aka sace ba a cewar Lai Mohammed. Channels TV ta rahoto cewa ya ce gwamnati za ta yi amfani da hanyoyi daban-daban don neman a saki daliban 



Ministan ya kuma nace cewa ba a biya fansa ba don sakin ‘yan makarantar Kankara da aka sace a jihar Katsina da kuma‘ yan matan makarantar Dapchi da ke jihar Yobe. 


Ya ce: "Muna amfani da dabaru daban-daban, ba ka watsi da gayyatar tattaunawa amma mutum kan boyewa zuciyarsa manyan dabarun da yake da su." Da yake ci gaba da bayani, ya ce, “ Yan fashi a duk duniya suna aiki da ilimin halin mutane. Da gangan, suke dana tarkonsu a kan mata da yara saboda wannan shine abin da zai jawo hankalin duniya sosai. Wannan shine ainihin abin da yan fashi suke yi a duk duniya." 


No comments:

Post a Comment

Pages