Bidiyon sojojin Najeriya yayin da suka kwace gonar Shekau a dajin Sambisa
- Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kai mamaya wata gona da ake zargin ta shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ce
- A cikin wani bidiyo da ya bayyana na sojojin, an jiyo su suna yi wa Shekau shagube a kan ya fito daga maboyarsa
- Hakazalika an gano wasu yan fararen hula suna kwasar amfanin gonar wacce ke a cikin dajin Sambisa Dakarun sojojin Najeriya sun mamaye wata gona da ake zargin mallakar Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ce a dajin Sambisa. A cikin wani bidiyo da jaridar PRNigeria ta saki, an gano yadda sojojin suka afka wa gonar tare da wasu yan fararen hula suna kwasar amfanin gona. An jiyo sojojin suna yi wa shugaban yan ta’addan ba'a sannan suka nemi da ya fito daga inda ya buya.
Sojojin sun ce: “Shekau ina kake sarkin ɓaɓatu, ga mu a gonarka za mu yi sallar Juma’a a cikin Sambisa. “Ba ka ce za ka yi shahada ba, ka fito mu barar da kai.” A halin da ake ciki, sojojin Najeriya a Dikwa bayan dakile harin da ISWAP suka yi, sun kama wasu maza biyu da ake zargi da yi wa 'yan ta'adda leken asiri a cikin al'umma.
No comments:
Post a Comment