Gwamnatin jihar Borno da ke Najeriya ta ce gwamnan jihar Babagana Zulum ba ya cikin tawagar da ta yi hatsarin da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane a kan hanyar Mafa zuwa Maiduguri.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Isa Gusau ya fitar ta ce kodayake wani makusancinsa yana cikin mutanen da suka mutu a yayin hatsarin, amma shi gwamnan ba ya cikin tawagar.
Ya ce mutanen da suka yi hatsarin sun bar gwamnan a garin Mafa inda suka yi gaba.
Ya kara da cewa sai dai yayin da tasa tawagar ta taso ta zo ta samu hatsarin har ma ta kwashi gawarwakin.
Cikin mutanen da suka mutu har Mai Kanuribe na Lagos, Mai Mohammed Mustapha da abokinsa da kuma direbansa.
Gwamnan tare da Sanata Kashim Shettima da wasu shugabanni, sun taras an yi hatsarin a kan hanyarsu ta dawowa daga Mafa kuma kamar yadda ya kamata, gwamna da mutanen da ke yi masa rakiya, sun raka gawar Mai da ta sauran mutanen da suka mutu, zuwa wurin iyalansu a Maiduguri, inda suka yi musu jaje sannan suka jalarci jana'izarsu," a cewar sanarwar.

No comments:
Post a Comment