Wednesday, February 10, 2021

Yadda hoton 'batsa' ya kawo ɓaraka a sabuwar gwamnatin Sudan

 



A jerin wasiƙunmu daga ƴan jaridar Afrika, wata marubuciya yar Sudan Zeinab Mohammed Salih ta yi waiwaye, wanda masu salon magana ke cewa adon tafiya kan tataɓurzar da ake yi a Sudan, dangane da irin darussan da suka kamata a koyar da yara ɗalibai bayan juyin juya hali. 


Bayan kwashe tsawon lokaci ana murna sakamakon hamɓarar da tsohon shugaban ƙasar Sudan Omar al-Bashir, a yanzu an mayar da hankali a kan fatan yin garambawul ga tsarin dimukraɗiyyar ƙasar.

Amma wani rikici a tsakanin manyan malaman addini dangane da sabon tsarin karatu a makarantu na nuna irin haɗarin da gwamnatin riƙon ƙwarya ke fuskanta.

Yayin sallar Juma'a a wani masallaci a babban birnin ƙasar Khartoum a makon da ya gabata, wani limami ya yi ihu cikin tsananin ɓacin rai da murya mai ƙarfi yana faɗin "Allah, Allah, Allah", sannan ya yi kira ga masallata su haɗa kai da gwiwa su yi kukan takaici, a kan yadda aka sanya hoton Michelangelo na Halittar Adam a wani littafin tarihi na rayuwa bayan juyin juya hali. 

Imam Mohamed al-Amin Isma'il, wanda ya kasance mai goyon bayan Bashir, ya yi imanin cewa hoton ƴan bidi'a ne, wanda za a iya kallo a matsayin na batsa.

Ya kuma caccaki SUNA, wato kamfanin dillacin labarai na gwamnati, saboda ba da wani dandali ga Omer al-Qarray, ɗaya daga cikin mutanen da ke goyon bayan wannan sabon shiri na kawo sauyi a tsarin makarantu, inda ya zarge shi da yaɗa kafirci da aƙidar mulhidanci.

Biyo bayan wannan suka da limamin ya yi, da yawa wasu limamai masu goyon bayan Bashir sun bi sahunsa don fara adawa da sabon tsarin karatun da shi kansa Mr Qarray daga baya danginsa suka ce sun samu saƙonnin barazanar kisa a kai.

Daga baya firaminista Abdalla Hamdok ya hana gabatar da sabon tsarin karatun, sakamakon matsin lamba. 

Mista Qarray, wanda ɗan ƙungiyar ƴan uwa Musulmai ta masu kishin ƙasa ne, ya yi murabus daga aikin tsara manhajar makarantu don nuna fushi da adawa a kan matakin firaministan.

Yana ganin cewa ya watsa masa ƙasa a ido, shi da wasu sauran jam'iyyun siyasa, don saurarar masu tsattsauran ra'ayi da ƙungiyoyin addinin Islama masu goyon bayan Bashir.

Haka kuma an samu saɓani kan yadda za a gabatar da abubuwan da suka shafi tarihin ƙarni na 19 na Sudan.






No comments:

Post a Comment

Pages