Wani rahoto da jaridar The Cable ta fitar ya nuna cewa Legas ta kasance yankin Najeriya mafi soyuwa ga masu saka hannun jari yayin da take kan gaba a jerin jihohin da suka fi jawo hankulan masu saka jari a shekarar 2020. Har ila yau bisa rahoton jihar Lagas din ta zarce sauran jihohin kasar ciki harda Babban Birnin Tarayya, Abuja. Legit.ng ta lura cewa rahoton wanda ya ambaci Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) a matsayin tushensa, ya nuna cewa Legas, cibiyar kula da tattalin arzikin Najeriya, ta jawo dala biliyan 8.31 a hannun jari.
Wannan ya wakilci kaso 85.7 na jimillar jarin da ya shigo kasar nan a shekara ta 202 Kalli jerin jihohin a kasa:
1. Lagos - $ 8.31 biliyan
2. Abuja (FCT) - dala biliyan 1.27
3. Abia - $ 56.07 miliyan
4. Niger - $ 16.36 miliyan
5. Ogun - $ 13.39 miliyan
6. Anambra - $ 10.02 miliyan
7. Kaduna - $ 4.03 miliyan
8. Sakkwato - $ 2.50 miliyan
9. Kano - $ 2.38 miliyan
10. Akwa Ibom - $ 1.05 miliyan
A wani labarin, Kungiyar yan kwadago TUC ta caccaki gwamnatin tarayya kan sabon shirin da take yi na kara farashin man fetur sakamakon karuwan farashin danyen mai zuwa $60 ga ganga a kasuwan duniya. TUC ta bayyana cewa gwamnatin nan ba ta tausayin yan Najeriya gaba daya, The Nation ta ruwaito.
A jawabin da shugaban kungiyar, Kwanred Quadri Olaleye, ya saki, ya ce gwamnati na azarbabin fadawa Najeriya farashi zai tashi amma ba ta gaggawa wajen cika alkawuranta.

No comments:
Post a Comment