Gwamnatin tarayya ta ci gaba da tattaunawa da ma’aikatan jami’ar da ke yajin aiki
- Ma’aikatar kwadago na da kwarin gwiwar cewa za a warware takaddamar da ke tsakaninsu da kungiyoyin
- Ma’aikatan da ke yajin aiki na korafi ne kan tsarin da gwamnatin tarayya ta dauka wajen biyan mambobinta albashi Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa harkokin karatu a jami’o’in gwamnati za su ci gaba nan ba da jimawa ba bayan yarjejeniyar da ta cimma tare da ma’aikatan jami’ar da ke yajin aiki.
A cewar jaridar The Nation, ma'aikatar kwadago da daukar ma’aikata ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, 12 ga watan Fabrairu.
Gwamnatin ta yi bayanin cewa ta cimma yarjejeniya tare da shugabannin kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya da na ma’aikatan jami’o’i(NASU), da nufin kawo karshen yajin aikin a ranar 15 ga Fabrairu. Mahukuntan sun ce rahotannin kafafen yada labarai wanda ke ikirarin cewa ganawar da aka yi tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadagon a ranar 11 ga watan Fabrairu ba ta haifar da ‘da mai idanu ba, ba gaskiya bane. Sanarwar ta karanto cewa: “Ganawar ba ta ƙare a rashin dadin rai ba.
Maimakon haka, an cimma yarjejeniya kan wasu batutuwa kuma an rubuta su a matsayin Yarjejeniyar fahimta sannan aka ba shugabannin kungiyoyin kwadagon biyu su je su tuntubi mutanensu da nufin dakatar da yajin aikin zuwa ranar Litinin, 15 ga Fabrairu, 2021.”
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa kungiyoyin kwadagon sun fara yajin aiki ne a kan yadda gwamnati ke tafiyar da tsarin biyan albashin ma’aikata na bai daya (IPPIS) da sauran batutuwa.

No comments:
Post a Comment