Selvarani Kanagarasu mace ce da take aikin leburanci a jihar Tamil Nadu da ke kudancin Indiya, inda ta kaurace wa aure don ta samu damar kula da bijimin Sa.
Ms Kanagarasu mai shekara 48 ta fada wa Wakiliyar BBC a Indiya Pramila Krishnan cewa ita kadai ce matashiya a lokacin da ta yanke shawarar bin sahun mahaifinta da kakanta na shiga aikin kula da bijimin, wanda ya lashe gasar wasannin gargajiya da ake yi a kasar wacce aka fi sani da Jallikattu.
Wasan Jallikattu ya shahara tun tsawon shekaru da dama a Tamil Nadu kuma suna yin wannan al'adar ne a lokacin bikin girbe amfanin gona na Pongal a watan Janairu.
Tsawon shekara biyu ke nan ba a gudanar da bikin wannan wasa ba, bayan da kotun kolin kasar ta haramta wasan a filin dabbobi. Sai dai zanga-zangar da aka yi kasar ne ya sa gwamnatin tarayya ta shirya dawo da shi a watan Janairun 2017.
"Babana da kakana dukkansu sun rungumi bijimin kuma suna kallon shi tamkar dan da suka haifa", In ji ta.
Za a ci gaba da yin wannana al'ada har zuwa kan 'yan'uwan Ms Kanagarasu, sai dai ta ce ba su da lokacin da za su kula da dabbobin, saboda haka ne ta yi shawarar ta karbi aikin. Sunan bijimin da take kula da shi Ramu mai shekara 18, wanda ya ke da kima a yankin Jallikattu.
Ramu ya lashe gasa biyar daga cikin bakwai da aka yi a gasar Jallikattu.
"Ramu tamkar da ne a wurina. Ya lashe kyautuka da dama, amma kyauta mafi girma da ya lashe ita ce mafi darajar zuri'ata a kauyen, ta kara da cewa ana matukar kaunar Ramu, duk da yanayin girman da yake da shi da kuma yanayin shi a lokacin gasar Jallikattu.
Ta saye shi lokacin yana da shekara 10. Tun da farko mai shi ya bukaci kudi masu yawa, amma ya amince ya sallama ma ta Ramu a kan kudi kadan, bayan da ta shaida ma sa cewa tana so ta rike shi amma kuma ba ta da halin wannan kudin da yake bukata.
Shawarar da MS Kanagaru ta yanke na kula da bijimin maimakon yin aure abu ne da ba a saba ganin shi ba, musamman a yankin kauyukan Indiya. Ta ce da farko 'yan uwanta da iyalanta ba su amince ba, amma daga baya sun amince da bukatarta.
Kuma wanann namijin kokari da ta yi na sadaukar da lokacinta ya janyo mata daraja da kima a cikin zuri'arsu da kuma sauran mutanen garinsu, inda take kula da bijimin duk da cewa abun da take samu bai taka kara ya karya ba.
Gidanta dan karami ne mai daki daya da wajen dafa abinci. Kudin Indiya rufi 200 kawai take samu a rana (kwatankwacin Naira 1,127 a kudin Najeriya), inda kuma take amfani da kusan dukkanin kudin a kan Ramu don ta tabbatar da lafiyarsa.
Gasar da Ramu yake shiga ne yasa yake bukatar abinci mai gina jiki. Bayan abincin da yawancin dabbobin Tamil Nadu suke ci, har ila yau kuma yana cin kwakwa, da dabino, da ayaba, da kuli-kuli, da gero da kuma shinkafa.
Ta ce, "Akwai lokacin da sau daya kawai nake cin abinci a rana don na adana kudin da zan siya wa Ramu abinci".
Baya da abinci mai gina jiki na musamman, Ramu na bukatar yin atisaye kodayaushe. Saboda haka kowacce rana Ms Kanagarus na fita da shi wajen gari inda zai yi ninkaya ya kuma wasa jini.
"'Yar'uwata Rajkumar ita ma na fita da shi yin atisaye. Kuma na samu rahoton ingancin lafiyarsa daga likitan dabbobi, saboda duk lokacin da za a shiga gasar Jallikattu ina tabbatar da ingancin lafiyarsa da kuma cancantarsa". In ji ta.
Daya daga cikin 'yan uwanta Indira Selvaraj ta ce mun yi mata tayin kudin Indiya sama da rufi 100,000 a kan ta bar Ramu.
Ta kara da cewa, "Tana da sha'awar kula da bijimin. Shirye-shiryen da take wa Ramu na shiga wasannin gasa shi ne kadai burinta a rayuwa. Mun kasa janye hankalinta daga kanshi. Yanzu ma kawai mun hakura mun sallama saboda idan mutum ya kwallafa ranshi akan abu ba yadda za ka yi da shi.
Kodayake ba ta da 'ya'ya, Ms Kanagarusu ba ta da niyyar barin wannna al'adar.
Yanzu haka ma tana koya wa wata 'yar uwarta mai shekara 18 Devadharshini yadda za ta gaje ta. Kodayake Devadharshini tana cewa ta san yadda za ta kula da Ramu, ba kuma tilasta ta aka yi a kan hakan ba, ita take so ta dawwama a kan hakan har karshen rayuwarta.
No comments:
Post a Comment