Saturday, February 13, 2021

(Bidiyo)Babbar magana: An kama ango yana lalata da kawar amarya a ranar daurin aurensu

 Babbar magana: An kama ango yana lalata da kawar amarya a ranar daurin aurensu 



Wani abun al'ajabi ya afku a garin Port Harcourt inda aka kama ango yana tarawa da kawar amarya a ranar daurin aurensu

A cikin wani bidiyo da ya bazu a yanar gizo, an gano amaryar tana caccakar wanda ya kamata ya zama angon nata, inda ta bayyana cewa shine umul'aba'isin rusa farin cikinsu 


Har ila yau abokan angon sun nuna rashin jin dadinsa yayinda suka daura laifin komai a kan abokin nasu

Wani aure ya mutu tun kafin a kai ga daura shi bayan amaryar ta gano cewa mijinta na mu’amala da babbar kawarta, jaridar The Nation ta ruwaito.

A bisa ga rahoton kafafen sadarwa, rigima ta barke a birnin Port Harcourt yayinda amaryar ta yiwa angon wankin babban bargo a tsakiyar hanya tana mai zarginsa da rushe auren.

A cikin bidiyon wanda ya bazu a dandalin sada zamunta, an jiyo abokan angon suna fadin cewa ‘ka kwafsa’ bayan sun tabbatar da aikata ta’asar. 

Ga Bidiyon a kasa




No comments:

Post a Comment

Pages