Budurwar, wacce mai bautar kasa ce a jihar Akwa Ibom, ta sha duka da zagi, yayin da samarin suke zarginta da kashe wani saurayi da ya kwana da ita - Ana zargin budurwar da kashe saurayin ne a dakinsa, yayin da tace yayi yunkurin yi mata fyade, amma kowa yayi ta musanta hakan Wata matashiya mai bautar kasa a jihar Akwa Ibom ta sha duka kamar bakuwar karya a ranar Lahadi.
Baya ga dukan, har tsirara wasu samari suka yi mata, suna zarginta da kashe wani mutum bayan ya kwana da ita. An ga bidiyon matashiyar, mai suna Odume Paschaline, ta kammala karatunta a jami'ar Najeriya dake Nsukka, tsirara haihuwar uwarta, maza suna dukanta da kuma zaginta.
Alamu sun nuna a tsakar anguwa ne al'amarin ya faru. A wani bidiyo da aka tura wa Premium Times ta WhatsApp, wanda wani mutum da lamarin ya faru gaban shi ya kwashe tas a wayarsa, an ga yadda samarin suka tozarta budurwar .
Bayan 'yan sanda sun isa wurin ne suka ceci matar, inda suka tafi da ita a motarsu. An ga hotunan wanda aka kashe male-male cikin jini a dakinsa. Mutane sun taru a anguwar suna tattaunawa akan yadda za su bullo wa lamarin.
Wata majiya ta tabbatar da cewa matar tana hannun 'yan sanda, kuma tayi ikirarin ya yi yunkurin yi mata fyade ne, shiyasa tayi kokarin ceton kanta da kanta. Kamar yadda majiyar tace, "Budurwar har gidan saurayin taje, da kamar a gidanta ne lamarin ya faru da da sauki." Sai dai, an ga yadda Paschaline ta kwatanta kanta a shafinta na Facebook, inda tace lallai tana da zuciya mai kyau, amma bata daukar shirme komai kankantarsa.


No comments:
Post a Comment