Monday, January 11, 2021

Ahmed Musa ya sha raddi bayan yada wasu hotunansa da matarsa a dandalin sada zumunta

 



Wasu mabiyan dan wasan kwallon kafa ta kungiyar Super Eagles, Ahmed Musa, sun nemi ya cire hotonsa da ya saka tare da matarsa


 - Ahmed Musa ya saka hotonsa tare da matarsa ta na sumbatar kuncinsa cikin farinciki da annashuwa 


- Sai dai, wasu mabiyansa sun ce hakan ya ci karo tare da sabawa tarbiyar addinin Musulunci Kwararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa, Ahmed Musa, ya sha suka tare da nasihohi da bayar da shawara a kan yada hotunansa tare da matarsa a dandalin sada zumunta. 


Sai dai, bayan dan wasan ya saka hoton a shafinsa na sada zumunta, wasu mabiyansa sun nuna rashin jin dadinsu tare da neman ya cire hoton saboda, a cewarsu, ya sabawa tarbiyar addinin Musulunci. 


Ga yadda wasu mabiyansa suka mayar martanta akan hoton 





No comments:

Post a Comment

Pages