Wani mutum ya tsallake rijiya da baya, inda ya tsira da rayuwarsa bayan da matarsa ta cizge masa maraina ta karfin tsiya.
Wannan lamari dai ya faru ne a jihar Osun kamar yadda kakakin rundunar askarawan kare fararen hula na Civil Defence, Daniel Adigun ya bayyana.
Kakakin na Civil Defence ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a garin Iragbaji da ke a karamar hukumar Boripe ta jihar Osun.
Matar mai suna Omolara Seriki mai shekaru 35 ta kaiwa mijinta, Raheem Serike mai shekaru 52, farmaki ne da misalin karfe 10:00 na daren jiya Talata, a wata maboya, inda ta iske shi da wata mace a cikin daki a maboyar tasa.
Kodayake dai shi Raheem ya bayyana cewa matar da mai dakinsa ta iske tare da shi a wannan maboya ba wai ta zo ne da nufin su aikata wani mummunan aiki ba, face abincin sayarwa da ta kawo masa, kuma bayan zuwan nata sai ruwan sama ya tsuge ya hana ta tafiya, shi ma ya hana shi tafiya gidansa.
Sai dai suna zaune suna jira ruwan ya dauke ne sai matarsa ta shigo dakin, inda da shigarta sai wajen ya yamutse, kuma a wannan lokacin ne ta samu hannunta ya kai kan marainansa, kuma bata yi wata-wata ba ta cizgesu.
Raheem ya ci gaba da cewa shi dai tun da ta fara fizgar marainan nasa ya fita daga hayyacinsa ya fadi a sume kuma bai farka ba sai a kan gadon asibiti, inda ya ga har an dinke marainan nasa da mai dakinsa ta cizge.
Majiyarmu ta gano cewa dama dai akwai wata a kasa tsakanin Raheem da mai dakinsa, Omolara wanda suka shafe shekaru 6 a matasayin mata da miji.

No comments:
Post a Comment