Saturday, January 2, 2021

Kano: 'Yan sanda sun kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)

 

Kano: 'Yan sanda sun kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)



Wani aljani ya fada komar rundunar 'yan sandan jihar Kano bayan wani matashi mai suna Aliyu ya shigar da kararsa 

Aliyu ya bayyana cewa aljani ta waya ya fara kiransa tare da bashi tsoro kimanin shekaru uku da suka gabata

- An samu kudin bogi da wasu kayan tsatsiba a wurin aljanin da aka kama wanda kuma shine ya ke kiran Aliyu tare da tilasta shi yi wa aljanu hidima

Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta samu nasarar kama wani aljani bayan wani matashi mai suna Aliyu Haruna Usman ya shigar da kararsa.

A wani faifan bidiyo da kakakin rundunar rundunar 'yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi magana, mai korafi ya bayyana yadda abin ya faru.

DSP Kiyawa ya bayyana cewa mai korafin ya shafe tsawon shekaru uku yana hidimatawa wannan aljani ta hanyar yi masa dafgen naman kan shanu, farfesun kaji, kindirmo.


Da yake magana da bakinsa a cikin faifan bidiyon, Aliyu ya bayyana cewa a wasu lokutan akan sanar da shi cewa 'ya'yan aljanu sun raina kayan alatun da ya kawo. 


A cewarsa, aljanin; wanda ya fara kiransa ta lambar waya, ya tsoratar da shi idan bai yi abinda aljanu suke so ba za'a kone masa gida ko kuma ya mutu.

Kazalika, ya sanar da cewa aljanin ya shaida masa cewa idan ya jure, ya cigaba da yin hidima zasu yi masa sakayya, su azurta shi.

Ga bidiyon a kasa


<blockquote class="twitter-tweet"><p lang="und" dir="ltr">Wani yakai karar Aljani a police station dake kano Kuma police sun kamo Aljanin 🤣🤣🤣<a href="https://t.co/rbAIxKHDkW">pic.twitter.com/rbAIxKHDkW</a></p>&mdash; Arewa Cycle (@arewacycle) <a href="https://twitter.com/arewacycle/status/1344967579450957830?ref_src=twsrc%5Etfw">January 1, 2021</a></blockquote> <script async src="https://platform.twitter.com/widgets.js" charset="utf-8"></script>


https://twitter.com/arewacycle/status/1344967579450957830?ref_src=twsrc%5Etfw%7Ctwcamp%5Etweetembed%7Ctwterm%5E1344967579450957830%7Ctwgr%5E%7Ctwcon%5Es1_&ref_url=https%3A%2F%2Fd-9911477693574790896.ampproject.net%2F2011252111003%2Fframe.html

No comments:

Post a Comment

Pages