- Kamar yadda katin daurin auren ya nuna, za a daura auren ne a yau Asabar 9 ga watan Janairu
- Wata Hajiya Kande daga karamar hukumar Wushihi na Jihar Niger ne ta dauki nauyin yin katin gayyatar Wani kafar watsa labarai na yanar gizo a Jihar Niger ya wallafa wannan hoton gayyatar daurin aure wani mutum dan shekaru 83 mai suna Alhaji Yushu'a Suleiman da wata yarinya, Amina Mohammed da aka ce shekarunta 16.
A takardan gayyatar, an shirya daurin auren ne a ranar Asabar 9 ga watan Janairun 2021, amma, ba a bayyana Jihar da za a daura auren ba.
Wata Hajiya Kande daga karamar hukumar Wushishi na Jihar Niger ne ta dauki nauyin yin katin gayyatar daurin auren.
Kamar yadda ya ke a hoton, dattijon na sanye da fararen kaya da rawani da tabarau yayin da ita kuma yarinya tana sanye da atampa.
Babu lambar wayar wasu daga cikin masu dawainiyar daurin auren kamar yadda aka saba saka wa a katin wasu gayyatan sai dai lambar wadanda suka buga katin shima bai fito da kyau ba saboda yanayin daukan hoton.
A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.
A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa. Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

No comments:
Post a Comment