Saturday, January 9, 2021

Korona: Buhari ya lissafo jerin manyan yan Najeriya da za su karbi allurar rigakafi kai tsaye a akwatin talbijin

 



- Za a nuno wasu jerin manyan yan Najeriya kai tsaye a akwatin talbijin yayinda suke karbar allurar rigakafin korona 


- Shugaba Buhari ya yarda ayi wa manyan yan Najeriya da dama a bangaren addini, wasanni da nishadantarwa allurar kowa ya gani 


- Gwamna Fayemi na Ekiti ya ce an yi hakan ne domin karfafa wa jama’a gwiwar karbar rigakafin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana so Limamai, manyan fastoci, manyan mawaka da yan wasanni a kasar su karbi allurar rigakafin korona kai tsaye a akwatin talbijin. 


Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar Shugaban kasa bayan ganawa da shugabannin Najeriya a ranar Juma’a, 8 ga watan Janairu a Abuja. 


A cewar wani rahoto daga jaridar Daily Sun, Gwamna Fayemi ya ce shugaba Buhari na so kwamitin fadar shugaban kasa kan korona ya kara manyan yan Najeriya cikin jerin wadanda za su karbi rigakafin kai tsaye a akwatin talbijin. 


Fayemi ya ce: “Shugaban kasa ya yarda da ni cewa zai sanar da kwamitin PTF fa’idar amfani da sauran masu fada aji, imma manyan Limamai, fastoci, manyan mawaka da yan wasan kwallon kafa. “Saboda ganin irin wadannan mutane suna karbar rigakafin zai sa ya kara karbuwa a garuruwanmu." 


No comments:

Post a Comment

Pages