Sunday, January 3, 2021

(Hotuna) Kudi Masu Gidan Rana Wani Dattijo Yayi Wuff Da Wata Tsaleliyar Budurwa

 



A farkon shigowar wannan sabuwar shekara ta 2021 wasu hotuna sun karade tare da zagaye kafar sada zumunta na wani abin sha’awa wanda wata shantalelliyar Budurwa zata auri ko ta aure wani wanda ya kai warin mahaifinta. 


Hakan dai bakomai bane a al’adar malam bahaushe uwa uba addininmu baiyi hani ba.

Ana dai ta kara samun dattijai masu abin hannu da suke zuwa suna aure yanmata masu karancin shekaru saboda abin hannun da suke da shi. Irin wadanann aurarraki har lakabin ‘Wuff’ ake masu. 


Ba ga maza kadai ba har matan da suka kwana biyu su kan zabi samari masu jini a jika su aure.

Ita kam in sha Allah ta fita daga layin yan mata masu neman mazan aure a kafar sada zumunta.


No comments:

Post a Comment

Pages