Monday, January 11, 2021

Hotuna: FG ta sa hannu kan kwangilar gina titin jirgin kasa daga Kano-Maradi da Kano-Dutse

 



- Gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan kwangilar gina titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi da kuma daga Kano zuwa Dutse 


- Minsitan sufuri, Rotimi Amaechi, ne ya saka hannu akan kwangilar da aka bawa wani kamfani mai suna Mota-Engil Group 


- Kamfanin Mota-Engil Group ya dauki gina jami'a kafin ya kammala aikin a matsayin tukuicin aikin da zai yi a Nigeria Gwamnatin tarayya, a ranar Litinin, 11 ga watan Janairu, 2021, ta rattaba hannu akan bayar da kwagilar gina titin jirgin kasa na zamani daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar da kuma daga Kano zuwa Dutse, babbn birnin jihar Jigawa. 


Kamfanin da aka bawa kwangilar aikin, Mota-Engil Group, ya dauki alkawarin ginawa Nigeria Jami'a kyauta kafin kammala kwangilar da aka bashi. 


Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ne ya sanar da hakan yayin da ya wallfa hotunansa yayin saka hannu akan kwangilar a shafinsa na dandalin sada zumunta. 


Fara sintirin jiragen a tsakanin Ibadan da Legas ya saka farinciki a zukatan 'yan Nigeria da ke harkokinsu a tsakanin jihohin biyu da kuma matafiya da ke shan azaba kafin shiga Legas saboda cunkuson ababen hawa. A ranar Litinin ne Legit.ng ta rawaito cewa hukumar kula da harkar lafiya a matakin farko; NPHCD ta sanar da cewa nan bada dadewa za'a fara rabawa jihohi alluran rigakafi. 




No comments:

Post a Comment

Pages