
Batun cinikin bakin haure 'yan Afrika tamkar bayi a Libiya shi ne batun da ya dau hankalin kasashen Afrika da dama a 'yan kwanakin nan. Shugaban kungiyar tarayya Afrika ta AU Alpha Conde, ya yi tir da wannan mummunar harka. Shi kuwa shugaba Mahamadu Isufu na Nijar, ya bukaci babban taron AU da EU ya saka wannan batun cikin ajandar taron da za'a yi a kwanaki masu zuwa a Abidjan. A yayin da gwamnatin hadaka ta Libiya ta ce za ta binciki batun.



No comments:
Post a Comment