
Wasu jama'ar garin Ganjuwa dake karamar hukumar Ganjuwa cikin Jihar Bauci sun huce fushinsu akan dan majalisar jihar mai wakiltar Ganjuwa ta Gabas Honarabul Saleh Umar Nabayi bayan da ya je kauyen ta'aziyya.
Al'amarin dai ya faru ne a ranar lahadi da ta gabata. Dama mutanen garin suna cike da haushin dan majalisar kasancewar suna zargin tun lokacin kamfen a shekara ta 2015 basu kara jin duriyarsa ba gashi kuma babu abin daya tsinana a yankin.
Bayanai sun tabbatar da cewa isar Hon Saleh Nabayi ke da wuya jama'a suka fara ihu suna bamayi bamayi bamayi. Abu kamar wasa sai wasu gungun matasa da suka fusata suka ce sun bashi minti biyar ya fice daga garin. Ana cikin haka sai suka fara jifan dan majalisar da tawagarsa inda suka fasa gilas din motarsa wasu kuma 'yan tawagarsa suka samu kananan raunuka.
Lamarin ya takaita ne bayan da tsohon hakimin kasar Soro, Alhaji Muhammad Isah Baba ya yi ta bada baki ga matasan, kafin Hon Saleh Nabayi da tawagarsa suka fice daga garin.
Da fatan al'umma za su rika hakuri su daina taba lafiyar irin wadannan 'yan siyasa da basu tsinana komai ba su bari sai lokacin zabe ya zo su koya musu darasi a akwatin zabe.
©Zuma Times Hausa
No comments:
Post a Comment