Wednesday, November 22, 2017

Labari Cikin Hotuna :-Al'ummar Vadoma Masu Yatsu Biyu



A kasar Zimbabwe da ke yankin kudancin Afrika, akwai wasu mutane da ake kira da Vadoma 'yan kabilar Bantwana, wadanda akasarin su ke zaune a arewacin kasar, a yankin gabar kogin Zambezi.
Akwai wasu mutane a cikin wannan kabila da Allah ya yi musu wata irin halitta, ta manyan yatsu biyu a kafar su. Ma'ana ba su da yatsun tsakiya guda 3 a kafafun su, abin da ya sa ba sa iya sa takalmi. Kuma yatsu biyun da aka yi musu sun tankware zuwa ciki.
Duk da yake ba sa sanya takalmi, amma suna tafiya har da zurawa da gudu, amma wasu yanayin lankwashewar kafafun na wahalar da su. Sai dai kuma suna da wata baiwa ta saurin iya hawa bishiya, har ma biyan su ake yi su hau don saro abu.
Labarin kunne ya girmi kaka ya nuna cewa, dattijan wannan kabila na tutiya da cewa asalin kakannin su daga wata duniya suke mai suna Sirius, kuma su wadansu irin halittu ne masu tashi sama kamar tsuntsaye. Sun ce wai sun shigo wannan duniya ne shawagi sai suka ga wasu matan 'yan Adam har suka sa su sha'awa, sai suka rikide suka koma suffar mutane suka aure su.
Akwai wata doka da aka gindayawa masu irin wannan halittar a Vadoma, wadanda ke da yake ba a yi musu kallon nakasassu, amma ana hana musu auren wata kabila, sai dai su kadai masu yanayi daya. Hakan ya sa na su cika yawa ba, don ba sa yaduwa sosai.
Amma kuma hakan ya sa masu wannan siffar halitta suna karuwa a kai a kai.
Masana kimiyyar halittar dan Adam na ganin wannan yanayi na wadannan mutane na da nasaba da canjin kwayar halittar da ake cewa 'mutation' wanda yake haifar da haka, a dalilin wata illa da kwayar halittar chromosome na 7 a jikin dan Adam.
Akwai wasu mutane masu shigen halittar Vadoma da aka gani a yankin gabashin Shona Kalanga da ke saharar Kalahari, da ake kyautata zaton suna da alaka.
Dama masu hikimar magana na cewa, in da ranka za ka ga abu da yawa!

No comments:

Post a Comment

Pages