Da A Ce Ni Ne Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa (INEC) Da Tuni Na Dade Da Ruguza Jam'iyyar APC Saboda Ba Ta Cancanci Zama jam'iyya Ba, Inji Buba Galadima. Sanannen jigon nan na jam'iyyar APC dake mulki a Najeriya wato Injiniya Buba Galadima ya bayyana matukar damuwar sa a bisa yadda jam'iyyar ta kasa gudanar da taron kwamitinta amintattun ta kusan shekaru uku kenan bayan kafuwarta. "APC ba ta cancanci zama jam'iyya ba, tsarin mulkinta ya tanadi cewa sai kwamitin amintattu da kwamitin gudanarwa na kasa da kwamitin wakilan tsara manufofin jam'iyyar na kasa sun yi taro duk bayan wata uku. A cewar sa: "APC ba ta cancanci zama jam'iyya ba kwata-kwata. Ya cigaba da cewa tsarin mulkin jam'iyyar dai ya tanadi cewa kwamitin amintattu da kwamitin gudanarwa na kasa da kwamitin wakilan tsara manufofin jam'iyyar na kasa dole ne suyi yi taro akalla sau hudu a shekara.

No comments:
Post a Comment