Majiyar mu ta ruwaito Gbenga Daniel na fadin ya kai ziyarar ne ga IBB domin tattaunawa da shi game da muradinsa na yin takarar shugaban PDP, inda yace babu wani dan siyasa mai hankali da zai nemi wannan mukami ba tare da ya nemi sa albarka su IBB ba. Dayake nasa jawabin, IBB ya bayyana jin dadinsa da takarar Gbenga Daniel, inda yace “Nayi matukar farin ciki lokacin dana ji kana kokarin sadaukar da kanka ka tsaya takara, dama lokaci yayi da za’a ba matashi daman tsayawa takara.
Na san OGD sosai, kuma na san zai kai jam’iyyar PDP ga gaci, ina goyon bayanka, ina sa ran kai ne shugabana a jam’iyyance mai jiran gado.”
No comments:
Post a Comment