Tuesday, August 29, 2017

Yan sanda sun cafke masu farfesun kayan cikin Dan Adam


Yan sanda sun cafke masu farfesun kayan cikin Dan Adam Yan sanda sun kama wasu masu farfesun kayan cikin mutane - An kama masu laifin ne a jihar Ribas - Sun sace wani fasto sannan kuma suka kashe shi Rahotanni sun kawo cewa rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta yi ram da daya daga cikin masu garkuwa da kuma kisan jama’a Roland Peter da wasu mutane 22 a jihar Ribas ayayinda suke sarrafa farfesun kayan cikin wai fasto. Roland na daya daga cikin masu garkuwa da mutane, sannan kuma su kashe mutanen tare yin gunduwa gunduwa da namansu domin amfanin kansu.

A tun a watan Agusta a shekarar 2015 ne suka sacewani fasto mai suna Samuel Okpara sannan kuma suka kashe shi bayan ya share tsawon shekaru 2 a wajensu daga bisani suka hada farfesun kayan cikin faston.

Rundunar ‘yan sandan hedkwatar jihar Ribas dake fatakwal ne suka cafke Roland da mutane 22 bisa zargin garkuwa da mutane, kisa jama’a da yin gunduwa gunduwa tare da cin naman dam Adam.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mr Zaki Ahmed ya ce an kama mutane 22 ne da makamai, za a gurfanar dasu gaban kotu a yayin da su kuma zasu cigaba da gudanar da bincike

No comments:

Post a Comment

Pages