Majiyarmu dai ta samu cewa jarumar a cikin firar ta kuma shawarci sauran jarumai mata na masana'antar fim din a wannan lokaci da su kame kan su su kuma maida hankali sosai wajen gudanar da sana'ar ta su saboda a cewar ta lokacin 'ya mace a masana'antar dan karami ne. Haka ma dai jarumar Fati Ladan ta bayyana kuma cewa a ra'ayin ta yawan da 'yan matan fim din ne suka yi musamman ma yara masu kananan shekaru yake jawo kuruciya da yawa a masana'antar. Fati Ladan dai ta yi aure ne kimanin shekaru hudu da suka gabata inda Allah ya azurta ta da samun da namiji amma daga baya ya rasu.
No comments:
Post a Comment