"A yau mun kaddamar da sabuwar jam'iyyar al'umma. Alhamdulillah da wannan jam'iyya. Ita ce ci gaban Najeriya." Bayan watanni 7 da wannan kalamai, fastocin zaben shi a karkashin GPN sun bullo a yanar-gizo Fastar ta zo da kalamai: "Ku zabi Hamza Al-Mustapha a matsayin shugaban kasa a 2019: Mai hali na kwarai, mai aiki tukuru, wanda ya cancanta don ci gaban Nageriya." A shekarar 1998, an kama Al-Mustapha da zargin shi ya kashe Kudirat Abiola, matar marigayi Moshood Abiola, wanda shi yaci zaben shugaban kas na 1993, kafin Abacha yayi masa juyin mulki, kuma ya kulle shi. An yankewa Al-Mustapha hukuncin kisa ta hanyar rataya a babbar kotun kasa ta Legas a 2012, amma bayan ya daga karar zuwa kotun sake bincike (Court of Appeal), an sallame shi a kan ba'a samu hujjar shi ya kashe Kudirat Abiola ba.
naijhausa
No comments:
Post a Comment