Tuesday, October 3, 2017

Babbar Magana!! Mustapha ya fito takarar shugaban kasa a 2019


A hankali—a hankali masu neman kujerar shugaban kasa a 2019 sai bullowa suke - Da farko Atiku, sai Fayose, yanzu kuma Hamza Al-Mustapha - Ya kaddamar da sabuwar jam'iyyar Green Party of Nigeria (GPN) Kamar gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, fastocin Manjo Hamza al-Mustapha na fitowa takarar shugaban kasa a shekarar 2019 sun fara baiyana a Yanar-Gizo. In za'a tuna a 2013 cewa shi tsohon mai tsaron marigayin shugaban kasa, Janar Sani Abacha, ya baiyana cewa bai da sha'awar takarar mukami, amma daga bisani kuma sai ya fito ya yi maganar samar da sabuwar jam'iyya, Green Party of Nigeria (GPN)
"A yau mun kaddamar da sabuwar jam'iyyar al'umma. Alhamdulillah da wannan jam'iyya. Ita ce ci gaban Najeriya." Bayan watanni 7 da wannan kalamai, fastocin zaben shi a karkashin GPN sun bullo a yanar-gizo Fastar ta zo da kalamai: "Ku zabi Hamza Al-Mustapha a matsayin shugaban kasa a 2019: Mai hali na kwarai, mai aiki tukuru, wanda ya cancanta don ci gaban Nageriya." A shekarar 1998, an kama Al-Mustapha da zargin shi ya kashe Kudirat Abiola, matar marigayi Moshood Abiola, wanda shi yaci zaben shugaban kas na 1993, kafin Abacha yayi masa juyin mulki, kuma ya kulle shi.
An yankewa Al-Mustapha hukuncin kisa ta hanyar rataya a babbar kotun kasa ta Legas a 2012, amma bayan ya daga karar zuwa kotun sake bincike (Court of Appeal), an sallame shi a kan ba'a samu hujjar shi ya kashe Kudirat Abiola ba.

naijhausa

No comments:

Post a Comment

Pages