Wani mutumi mai suna Chidhatma Basu ya auri macen bera a Garin Bangalore na Kasar India bayan mai dakin sa ta rasu a farkon shekarar nan a wani hadarin mota. Mutuwar ta sa wannan mutumi mai shekaru 41 da 'ya 'ya 4 ya zama gwauro. Mista Basu yace wata rana yana zaune cikin takaici da maraici sai ga shi ya ga wata bera mai idanuwa da hanci sak na marigayiyar matar sa. Mutumin yace ya fahimci cewa matar sa ce kurum ta dawo daga irin abincin da take ci. Malamin da ya daura auren yace tabbas haka aka yi. Idan ba a manta ba bayan dawowar Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari sai daga gida yake aiki a wani ofishin sa saboda beraye sun fatattake sa.
No comments:
Post a Comment