Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo ya bayyana cewa idan Buhari zai kara tsayawa takara zai duba aikin da ya yi duka, daga su ne zai yanke hukunci a kan ko zai sake zabensa inda ya nuna cewa ya zabe shi shekara biyu da suka wuce ne saboda a lokacin zai iya zabar kowa amma fa ban da Goodluck Jonathan, Cif Obasonjo Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kokari idan aka yi la'akari da yadda ya samu nasara a bangare biyu wadanda ya fi kwarewa a kai inda ya fara magance matsalar cin hanci da rashawa da kuma yaki da masu tada kayar baya. Ya ci gaba da cewa ba zai taba yiwu ba a magance matsalar Boko Haram gaba daya, a tashi guda, "saboda manyan abubuwan da suka jawo ta kamar talauci da rashin aikin yi da jahilci har yanzu suna nan, ba a magance su ba," kamar yadda ya ce.

No comments:
Post a Comment