Sunday, September 10, 2017

Ina Adu'a Allah yasa man fetur din Najeriya bushe -Inji El-rufai


Ina Adu'a Allah yasa man fetur din Najeriya gushe - Dogaro da arzikin man fetur ya hana mu kirikiran sabin hanyoyin neman arziki - Hukumar yansandar Najeriya na bukatar karin ma'aiakata da mamakaman zamani dan Inganta tsaro Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El- Rufai, yace ya na rokon Allah yasa man fetur din Najeriya ya gushe. Yace dogaro da arzikin man fetur ke hana yan Najeriya kirkiran sabin hanyoyin neman arziki El-Rufai ya fadi haka ne a lokacin da ya halarci wani taron tuna marigayi Ojetunji Aboyade shahararren farfesa a fannin tattalin arziki a Ibadan a ranar Asabar 8 ga watan Satumba 2017.

Gwamnan yace "Duk lokacin da man fetur din Najeriya yakare, gwamanti da al’ummar kasar za su mai da hankali wajen ganin kasar ta cigaba.”

Saboda Najeriya tana samun arziki a sauwake ta dalilin man fetur, kasar ta daina tunanin yadda za ta samar da wasu hanyoyin kudaden shiga dan fadada tattalin arzikin kasar.” “Saboda muna samun kudi a cikin sauki, mun daina ansa haraji, mun daina mutunta masana da muke dasu a jami’o’In mu.” “Wannan abun bakin ciki ne, amma ina adu’a Allah yasa man ya gushe dan mu fara amfani da kwakwalwan mu, kuma mun daina ganin girman masu ilimi a cikin mu dan kudaden da muke samu a cikin sauki,” Inji El-Rufai. Akan batun yansada, El- Rufai yace: “Maganar gaskiya shine Najeriya ta na da karanci yansanda, hukumar tana bukata Karin ma’aikata da Karin makaman zamani kafin tsaro ya inganta a kasar.”

-Naijhausa

No comments:

Post a Comment

Pages