Saturday, September 9, 2017

BINCIKE: Farashin abinci ya fara sauka a kasuwanni jihohin kasarnan


Manoma musamman na yankin Arewa Maso Gabacin Najeriya sun ce farashin abinci ya fara sauka sannan za a ci gaba da samun hankan da zaran an fara girbin amfanin gona. Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ce manoman da suka yi noma bana musamman a jihohin Borno, Gombe, Bauchi, Adamawa and Jigawa za su sami yalwan amfanin gona saboda ba su fuskanci matsaloli a noma bana ba. Gidan jaridar ta gano hakan ne a wata binciken da ta gudanar akan aiyukkan noman bana. Binciken ya nuna cewa farashin buhun shinkafa(100kg) ta sauka daga Naira 34,500 zuwa 31,000 ko kuma kasa da hakan sannan tiyan shinkafa ta sauka daga Naira 1,100 zuwa 900. Sauran amfanin gonan da farashinsu ya sauka sun hada da wake,masara da gero. A jihar Borno wani Ali Muhammad wanda ke sana’ar siyar da shinkafa yace farashin kudin abinci bana na sauka a hankali. Ita kuwa Ya-Ana Kachalla wata manomiyar gyada ta ce hakan ya yiwu ne saboda taimako da suka samu daga wajen gwamnati. A jihar Gombe wani Shehu Abdulahi mai siyar da hatsi yace bana hatsi za ta sauka saboda yalwan amfanin gona. ‘‘ Yanzu ana samun buhun masara a farashin Naira 10,000 daga 17,000’’. A jihar Bauchi ana siyar da tiyan masara akan Naira 220,Dawa akan Naira 250,Shikafa akan Naira 450 da Wake akan Naira 400. Sakataran ma’aikatan aiyukkan noma na jihar Bauchi Bala Lukshi ya ce duk da cewa mafi yawan manoma basu fara girbe amfanin gonan su ba sai a karshen watan Satumba amma suna sa ran cewa farashin abinci zai kara sauka da zaran an girbe kayan abincin da aka fi bukata. A jihar Adamawa shugaban masu sana’ar siyar da hatsi Muhammadu Algarara ya ce farshin abinci a jihar bai sauka ba domin a yanzu hakan buhun shinkafa ana siyanta akan Naira 16,000 zuwa 17,000 sannan tiya ta kai Naira 450. Shuagaban kungiyar manoma na AFAN a Jigawa Maiungwa Jaga yace farashin abinci ya fara sauka a jihar. Ya ce manoman da suka noma kayan abinci kamar tumatir,ridi,wake,masara da sauran su za su sami yalwa bana.

No comments:

Post a Comment

Pages