Wani babban Jami'in Jam'iyyar Ahmad Lawan yace akwai garaje a kalaman Ministar harkokin matar kasar Aisha Jummai Alhassan da ta nuna goyon bayan ta a fili ga Atiku Abubakar alhali tana Minista a Gwamnatin Buhari. Lawan yace dama ta jira an kada gangar siyasar 2019 tukun. A game da zaben na 2019 Lawal yace idan har Shugaba Buhari ba zai tsaya takara ba ai akwai Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya san bakin zaren. Ya kara da cewa ba wai dole sai Shugaban ya fito daga Arewa ba don mulki na gari ake nema kurum. Kun dai ji bisa dukkan alamu tsohon Mataimakin Shugaban kasar nan Atiku Abubakar na da shirin takara amma da dama na Jama'ar kasar sun nuna rashin amincewar su da Atiku Abubakar.
No comments:
Post a Comment