Tuesday, April 13, 2021

Gaskiyar Maganar ! Shin Amurka Ta sanya Suna Isah Pantami Cikin Jerin Yan Ta’adda ?

 




Rahoton da wasu jaridun Najeriya suka wayi gari da shi ranar Litinin da ke ikirarin cewa Amurka ta sanya sunan ministan sadarwa Isa Ali Pantami a cikin jerin ‘yan ta’addan duniya ya ja hankalin ‘yan kasar.

Kodayake jaridun da suka wallafa rahoton ba sanannu ba ne, batun ya ja hankali sosai musamman a shafin Twitter inda ya kasance daya daga cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a kasu a shafin a yau Litinin.

Ratohon ya ambato wasu majiyoyin leken asirin Amurka suna cewa kafin nadinsa a matsayin minista, Isa Ali Pantami yana da tsattsauran ra’ayi game da Amurka sannan ya yi mubaya’a ga kungiyar Al-Qaeda.

Kazalika sun ambato wasu bayanai daga abin da suka kira majiyoyin leken asiri na Yammacin Duniya na cewa ministan ya yi alaka ta kut-da-kut da Muhammad Yusuf, shugaban kungiyar Boko Haram na farko kuma yana da dangantaka da Abu Qatada al-Filistini da kuma wasu shugabannin kungiyar Al-Qaeda da suka ce yana matukar girmamawa.

BBC Hausa ta tuntubi Pantami wanda ya musanta wadannan rahotanni.

Jaridar Daily Independent, wadda ita ta soma wallafa wannan labari, ta yi ikirarin cewa Minista Pantami a baya yana yaba wa Abu Musab Al-Zarqawi a matsayin babban shugaba, wanda ya shiga kungiyar Al-Qaeda bayan ya yi hijira zuwa Afghanistan bayan harin da aka kai a Amurka na ranar 11 ga watan Satumbar 2001.

Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wadannan bayanan da wannan jaridar ta wallafa.

‘Ana neman ɓata sunan Pantami’

 

Jaridun da suka wallafa wannan labari ba su fito fili sun bayyana majiyoyinsu ba lamarin da ya sa wasu ke kallon labarin a matsayin shaci-faɗi.

Binciken da BBC ta gudanar ya nuna cewa babu wata hukumar tsaron Amurka da ta sanya sunan ministan a cikin jerin ‘yan ta’adda na duniya.

Misali, a cikin jerin ‘yan ta’adda da hukumar leken asirin Amurka ta FBI ke nema ruwa ajallo, wanda ta wallafa a shafinta na intanet, babu minista Pantami.

Ita ma hukumar tsaron Amurka ba ta sanya sunansa a cikin wadanda ke daukar nauyin ta’addanci ko ma ‘yan ta’adda ba.

Mai magana da yawun Ministan, Misis Uwa Suleiman, ta shaida wa BBC Hausa cewa an buga labarin ne da zummar ɓata sunan ministan.

Ta ce wasu mutane ne da suka rasa yadda za su ɓullowa Pantami domin su muzanta shi – shi ne suka fake da ƙirƙirar labarin.

Haka kuma a shafinta na Twitter ta wallafa jerin sunayen mutanen da FBI take nema ruwa a jallo bisa zargin ta’addanci.

Isa Ali Pantami, malamin addinin Musulunci ne da ya yi karatunta a kasashe da dama ciki har da Saudiyya.

Tun bayan ɓullar Boko Haram, Pantami yake bayyana ƙyamarsa game da yadda take gudanar da ayyukanta, lamarin da ya sa ya taɓa yin muƙabala da shugaban ƙungiyar na farko Muhammad Yusuf inda ya ƙalubalance shi kan koyarwar ƙungiyar.

Shekau ya yi barazanar halaka Pantami

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

A shekarar 2020, shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi barazanar kashe minista Pantami.

A bidiyon da ya fitar na tsawon minti tara, ya ce ya yi barazana ga ministan ne saboda matsayinsa na malamin addini amma yana aiki na gwamnatin da ba ta musulunci ba.

Don haka binciken BBC Hausa na ya nuna cewa labarin da jaridun na Najeriya suka wallafa na alakanta Isa Ali Pantami da kungiyar Boko Haram ko kuma hukumomi a Amurka na nemansa bisa alaka da ta’addanci ba gaskiya ba ne.

No comments:

Post a Comment

Pages