Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da biyan kudi N13.9 million da kyautar mota ga Likita dan jihar Ogun, wanda ke ya cigaba da aiki a asibitin Monguno bayan shekaru shida da ritaya.
Gwamnan ya jinjinawa Likitan wanda ya cigaba da aiki babu albashi duk hadarin da ke Munguno sakamakon yakin Boko Haram. Zulum ya bayyana cewa Dr. Isa Akinbode ya kwashe shekaru 22 yana aiki a jihar Borno kafin yayi ritaya a 2016 a Asibitin Monguno.
Bayan ritayarsa, Likitan da Boko Haram suka taba sacewa a Monguno ya cigaba da aiki kyauta A baya, tsohon gwamna Kashim Shettima ya kai ziyara Monguno inda ya umurci ma'aikatan ma'aikatar umurnin daukan Dr Akinbode akan kwantaragi.
Amma saboda wasu dalilai, ma'aikatan har yau basu dauki Likitan ba amma duk da haka ya cigaba da aiki.
Bayan shekaru biyar, gwamna Zulum a ranar Juma'a ya bada umurin biyan Likitan kudin albashinsa tun daga lokacin da yayi ritaya a 2016 zuwa yanzu N13.9m.
Hakazlaika ya bada umurnin biyan Likitan kudin albashi kowani wata kamar yadda aka shar'anta a kwantiragin. Daga bisani gwamnan ya bashi kyauar mota Toyota Highlander kan ayyukan da ya yiwa al'ummar jihar Borno. "Mutane irin (Dr Akinbide) ya kamata a rika karawa karfin gwiwa, yana zaune a Monguno duk da matsalolin tsaro.
Magabaci na a ziyarar da ya kawo Monguno ya bada umurnin mayar da shi bakin aiki kan kwantiragi amma wasu dalilai ba'ayi ba," Zulum yace "Domin cika alkawarin maigidana, na yanke shawaran sake daukansa kwantiragi." "Zamu biya dukkan bashi albashin da yake binmu, zan bashi kudi N13.9m." Bayan haka, Zulum ya ce a dauki diyar Likitan aiki a daya daga cikin ma'aikatun jihar Borno.


No comments:
Post a Comment