Yaro Dan Shekara 12 Ya Kashe Budurwarsa A Jigawa
Wani matashi dan shekaru 12 mai suna Muhammadu Sani ya kashe budurwarsa mai shekaru 15 a kauyen Damutawa da ke karamar hukumar Jahun ta jihar Jigawa.
An yi zargin cewa Muhammadu ya halaka budurwar tasa mai suna Habiba Junaid a ranar Asabar da misalin karfe 2:00 na rana lokacin da take wasa a wajen kawunta, Legit ta ruwaito daga jaridar PMNews
Muhammadu ya dauki bindigar kawun nata sannan ya harbi Habiba a baya. A nan take ta mutu.
Kakakin yan sandan jihar Jigawa, ASP Zubairu Aminudeen Ismail ya tabbatar da lamarin inda ya ce bayan yan sanda sun samu labarin, sun yi gaggawan daukar ta zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta.
Kakakin yan sandan ya ce an kwato bindigar sannan aka kama wanda ake zargin yayinda har yanzu ake ci gaba da bincike.

No comments:
Post a Comment