Thursday, February 18, 2021

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya naɗa sabbin shugabanni a NSCDC da NCoS

 Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya naɗa sabbin shugabanni a NSCDC da NCoS 


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabin shugabanni a hukumomoin NSCDC da NCos

 - An nada Ahmed Abubakar Audi a matsayin sabon shugaban NSCDC yayin da ya zabi Halliru Nababa ya jagoranci NCoS

 - Sanarwar nadinsu ya fito ne ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida, Mohammed Manga, ta shafin Twitter na ma'aikatar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Ahmed Abubakar Audi a matsayin sabon babban kwamandan hukumar tsaro da NSCDC da aka fi sani da Civil Defence. 

Nadin na zuwa ne bayan murabus din da tsohon shugaban hukumar ta NSCDC, Abdullahi Gana Muhammadu ya yi. 
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, Mohammed Manga ne ya sanar da nadin cikin wata wallafa da ya yi ta hanyar amfani da shafin Twitter na ma'aikatar. 

Sanarwar ta ce, "Ahmed Audi ya zama zakara cikin wadanda aka yi wa gwaji domin tabbatar da tsarin adalci da @MinOfInteriorNG ta hannun kwamitin ta domin tabbatar da cewa wanda ya fi dacewa cikin jami'ai masu babban mukami ne ya maye gurbin shugaba mai barin garo. 

No comments:

Post a Comment

Pages