Sunday, February 21, 2021

Yanzu-yanzu: An sako ɗalibai da malaman makarantar GSS Kagara

 Yanzu-yanzu: An sako ɗalibai da malaman makarantar GSS Kagara 





- Sakatariyar watsa labarai na gwamnan jihar Niger, Mary Noel-Berje ta tabbatar da sakinsu inda ta ce suna hanyar zuwa Minna

- Mary Noel-Berje ta ce inda sun isa Minna babban birnin jihar Niger, gwamnan jihar Abubakar Sani-Bello zai tarbe su

An sako mutane 42 da yan bindiga suka sace daga kwallejin kimiyya na gwamnati da ke Kagara a jihar Niger, The Nation ta ruwaito.

Wadanda aka sace sun hada da dalibai 27, ma'aikata 3 da kuma iyalan ma'aikatan su 12.

Majiyoyi sun ce wadanda aka sace din suna kan hanyarsu na komawa Minna a yanzu. 


Kazalika, sakatariyar watsa labarai na gwamnan jihar Niger, Mary Noel-Berje ta tabbatarwa Premium Times cewa an sako su a daren yau Lahadi 21 ga watan Fabarairun 2021. 


Ta kara da cewa wadanda abin ya faru da su suna hanyarsu ta zuwa Minna, babban birnin jihar Niger gwamnan jihar Abubakar Sani-Bello zai tarbe su.

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

No comments:

Post a Comment

Pages