- Tsohon Shugaban ma’aikatan tsaro, Abayomi Olonisakin ya bayyana inda yakin Najeriya na gaba zai barke
- Olonisakin ya ce a bisa ga binciken da yayi shekaru uku da suka gaba, ya gano cewa Najeriya na da gandun daji sama da dubu wanda ya zama mafakar miyagun mutane
- Ya fadi hakan ne a yayin tantance shi da majalisar dokoki tayi don samun mukamin jakadanci Tsohon Shugaban ma’aikatan tsaro, Abayomi Olonisakin, a ranar Alhamis, 18 ga watan Fabrairu ya bayyana cewa yaki da rikice-rikicen Najeriya na gaba zai kasance a cikin dazuzzuka.
Janar din sojan mai ritaya, wanda ya yi murabus a matsayin babban Shugaban ma’aikatan tsaro a watan Janairun da ya gabata bayan shafe shekaru shida yana aiki a babban mukamin, ya yi wannan bayanin ne yayin da ake tantance shi a Majalisar Dokokin Tarayya.
Majalisar na tantance shi sakamakon aika sunansa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi zauren don nada shi mukamin jakadanci.
A cewar Olonisakin, wani bincike da ya gudanar a kan dazuzzuka shekaru uku da suka gabata ya nuna cewa Najeriya tana da gandun daji sama da dubu kuma akwai matukar bukatar mutum da kare gandun dajin wadanda suka zama maboyar masu aikata laifi. A bisa ga rahoton Bankin Duniya na 1992, gandun dajin Najeriya ya kai kashi 10 cikin dari na duk fadin kasar, Channels TV ta ruwaito.
Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, a watan Janairun da ya gabata ya umarci masu zama a dajin jihar ba bisa ka’ida ba da su bar gandun dajin, lamarin da ya haifar da cece-kuce.

No comments:
Post a Comment