Sanusi ya bukaci gwamnati ta kayyadewa 'yan Najeriya yawan iyalin da za su haifa
- Tubabben sarkin Kano, Sanusi II ya bukaci gwamnati da ta saka dokar kayyade yawan iyali
- Tsohon shugaban babban bankin ya ce hakan ne kawai zai kawo daidaituwar yawan 'yan Najeriya
- Muhammadu Sanusi ya ce ba Musulunci bane haifar yaran da ba za a iya kula da su da kyau ba Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yayi kira ga gwamnati da ta saka tsauraran dokoki da za su daidaita hauhawar yawan jama'a a kasar nan.
Sanusi wanda yayi magana a ranar Laraba yayin wani taro a Legas, ya ce ya dace jama'a su dinga haifar yaran da za su iya kula da su, Daily Trust ta wallafa.
Kamar yadda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya yace, abubuwan da ke bayyana a halin yanzu sun nuna cewa gwamnati ba za ta iya samar da dukkan ababen more rayuwa da ake bukata ba.
Sanusi ya kushe yadda ake haihuwa a kasar nan ba tare da karfin kula da yaran ba, wanda yace hakan ba daidai bane ko a addinin Musulunci. Ya ce: "Yadda jama'a ke auren duk yawan matan da suke so ba tare da wata dokar da ta gindaya yawan yaran da za a haifa ba bai dace ba ko a Musulunci. "Ban san dalili ba amma akwai doka a Musulunci da ta hana tara iyali ba tare da kayyade su ba. Babu wani tabbacin cewa za a iya kula dasu ba tare da an yi watsi da dawainiyarsu ba."
A wani labari na daban, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai samu damar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC ba a zaben shugaban kasa 2023.

No comments:
Post a Comment