Wednesday, February 17, 2021

Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'

 Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta' 





An umurci wata tsohuwar sarauniyar kyau ta yi murabus daga aikinta a asibiti saboda 'kyan ta ya yi yawa' kamar yadda LIB ta ruwaito. 


An nada Claudia Ardelean, mai shekaru 27 ta yi aiki a kwamitin asibitin Pneumophthisiology Clinical Hospital a kasar Romania duk da cewa ba za a rika biyanta albashi ba. Ardelean tana da digiri biyu a aikin lauya da nazarin al'adun turawa. 


Bayan samun aikin, ta yi farin ciki har ta wallafa a kafar sada zumunta a ranar 8 ga watan Fabarairu. 



Tsohuwar sarauniyar kyan ta wallafa hoton selfie da ta dauka a gaban ginin asibitin inda ta rubuta: "Ina godiya saboda gudunmawa da amintaka da na samu daga Cluj Nationtal Liberal Party!". 


Claudia wacce yanzu ta ke aiki a matsayin lauya a wani kamfanin kasar ba ta yi tsokaci game da ajiye aikinta na kwamitin asibitin ba. Shugaban Cluj Alin Tise ta amsa cewa ta cancani amma duk da hakan ta fitar da sanarwa cewa, "na yi nadamar abinda ya faru. "Na bukaci Claudia Ardelean ta yi murabus." 

No comments:

Post a Comment

Pages