Na Tumɓuke Sanusi Daga Sarauta Ne Saboda Bai Yi Kama Da Basarake Ba— Ganduje
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ya tumɓuke tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II daga sarauta ne saboda bai fahimci mene ne aikace-aikacen basarake ba.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da Gidan Talabijin na Channels a shirin Politics Today ranar Juma’a.
A ranar 9 ga Maris, 2020 ne Gwamnatin Jihar Kano ta sauke Muhammad Sanusi II daga sarauta, sakamakon zargin sa da rashin biyayya gare ta.
A cewar Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, SSG, Alhaji Usman Alhaji, taron tattaunawa na Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ya amince da sauke Sarkin ne nan take saboda ƙin biyayya ga umarnin da gwamnatin take ba shi.
Gwamna Ganduje ya yi zargin cewa tsohon Sarkin ya kasa sauyawa daga mai suka zuwa basarake.
Ya ce tsohon Sarkin ya manta ya “sa wa bakinsa linzami”, kuma yana lalata tsarin sarauta.
“Labarin gaskiya shi ne tsohon Sarkin Kano bai fahimci mene ne aikace-aikacen basarake ba, musamman ga muhimmiyar masarauta kamar ta Kano.
“Tsohon Sarkin Kano mutum ne mai suka, mutum mai suka da mutane suke jin daɗin abin da yake yi, kuma hakan ba laifi ba ne saboda mutum ne mai ilimi, akwai ‘yancin faɗar albarkacin baki.m”, in ji shi.
Gwamna Ganduje ya bayyana cewa lokacin da yake Mataimakin tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, a lokacin Sanusi yana Babban Darakta a wani banki, Kwankwaso ya ji haushi sakamakon wani furuci da Sanusin ya yi a kan gwamnatinsa.
“Shi (Sanusi) ya bayyana cewa maimakon mu samar da ruwa a jihar, mun tafi muna gina gidan alfarma a Abuja, gidan Gwamna da yake Asokoro.
“Na tuna lokacin da Gwamnana ya ce ko dai bankin ya sallame shi ko kuma mu kwashe kuɗaɗenmu daga asusun, bankin bai sallame shi ba, saboda haka muka kwashe miliyan N969 daga bankin. Wannan shi ne aikin mutum mai suka”, in ji Gwamna Ganduje.
Gwamnan ya ƙara da cewa lokacin da Sanusi ya zama Sarkin Kano, sai ya ƙi sauya halinsa zuwa na basarake.
“Masanin tattalin arziƙi ne amma ya kasa fahimtar cewa a tattalin arziƙi, dole ka gaji kadarori da haƙƙoƙi.
“Amma shi kadarorin masarautar kawai ya gada ta hanyar bada umarni, zama a gidan alfarma, sa kaya na ƙawa sai kuma a kira shi Sarki, amma ba mutuncin wannan masarautar ba— dole ka sa wa bakinka linzami, amma bai yi haka ba.
“Wannan ita ce matsalar. Wannan ita ce matsala mafi girma; ya kasa sauya ɗabi’arsa daga mai suka zuwa basarake”, a kalamansa.
Ganduje ya ƙara da cewa: “A yanzu masarautar ba ta son mutum mai suka irin tasa. Da matsalar da ake da ita a cikin al’umma, yana lalata masarautar ne. Shi yasa na samu matsala da shi; yana lalata masarautar ne”, ya ƙara da haka.

No comments:
Post a Comment